An kama matar ɗan ta'addan da 'Yansanda ke nema ruwa jallo da kuɗi sama da miliyan biyu a jikinta
An kama A'isha Nura matar wani ƙasurgumin ɗan ta'adda da 'Yansanda ke nema ruwa a jallo bayan ya aike ta ta amso mashi wasu kuɗaɗe da suka haura sama da naira milyan biyu a Kaduna yayin da shi kuma ya ke ci gaba da ɓuya a cikin dajin Batsari da ke jahar Katsina.